Kotun Shari'ar Musulunci ta dauki mataki kan Sheikh Idris Abdul'aziz.

Kotun Shari'ar Musulunci ta dauki mataki kan Sheikh Idris Abdul'aziz. 


Kotun Shari'ar Musulunci a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, ta mayar wa da waɗanda suka tsaya wa Dakta Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi takardun kadarorinsu da suka bayar domin karɓar belin shi da ta bayar a baya.


Wannan mataki dai na nufin kotun ta janye belin da ta bayar kan Dakta Idris, wanda kuma hakan yake nufi a kowanne lokaci za a iya kama shi.


Barista Ahmad Musa Umar shi ne lauyan da ke kare Dr Idris, ya ce "kotu za ta iya bai wa 'yan sanda takardar kama Dakta Idris a kowanne lokaci".


"Kotun ta ce ta ɗage shari'ar zuwa ranar 24 ga watan nan na Janairu, wanda kuma take tsammanin jami'an tsaro sukai mata shi gabanin wannan rana," in ji Barista Ahmad Musa.


Kotu ta yanke wa yar Amurka shekara 26 a kurkuku kan kisan mahaifiyarta

An gano sabon nau'in sauro da ke zagon-ƙasa ga yaƙi da Maleriya - WHO

NCC ta dakatar da shirin hana masu layin Glo kiran layin MTN

Kenya ta kama jami'an ƴan sanda bisa zargin sace wani ɗan ƙasar China

Rahoto kai-tsaye

Karin bayani

Rahoto kai-tsaye

Daga A'isha Babangida da Nabeela Mukhtar Uba


Ana dai tuhumar Dakta Idris ne da laifuka biyu, na farko kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.


Na biyu kuma ana tuhumarsa da laifin tayar da zaune tsaye.


Har yanzu dai ba a fara sauraran wannan shari'a ba kan waɗannan tuhume-tuhume.


Amma a baya ya yi zaman gidan kaso kan waɗannan tuhume-tuhume na tsawon kwana 39 tsakanin watan Yuni da Yuli, in ji lauyansa.


Ga Video Yadda aka kamashi👇


 

Previous Post Next Post